Dan takarar gwamnan jihar Kogi na jam’iyyar PDP, Sanata Dino Melaye, ya gabatar da jawabi ga manema labarai ana tsaka da kaɗa ƙuri’a a zaɓen gwamnan jihar.
Ana gudanarwa a wannan zaɓe ne a yau Asabar, inda ya zargi hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa INEC da yunkurin yi masa wala-wala.
Melaye ya ce dole INEC ta soke sakamakon zaɓen ƙananan hukumomi guda biyar, wadanda suka hada da Okene, Okehi, Ajaoukuta, Adavi da kuma Ogori/Mangogo.