Wasu da ake zargin yan bindiga sun kai farmaki fadar wani basarake, tare da sace shi da matarsa a ƙauyen Olayinka, da ke ƙaramar hukumar Ifelodun a Jihar Kwara.
Rahoton ya nuna cewa maharan sun kai farmaki fadar Oba Salman Aweda da misalin ƙarfe 1:40 na dare ranar Asabar, inda suka rika harbi sama domin tsoratar da mazauna yankin kafin su tafi da basaraken da matarsa da kuma mutum daya
Rahotanni na cewa kawo yanzu ba a san inda akai basaraken da sauran mutanen ba, amma hukumomin tsaro na ci gaba da gudanar da bincike kan lamari.
Karin bayani na tafe.
