A Lahadin nan China ta ce yawan kudin da take kashewa a fannin tsaro zai karu ainun a cikin shekaru 4 masu zuwa, tana mai kashedi a game da abin da ta kira da barazana daga waje.
Shugaban China Xi Jinping ne ya yi wannan bayani a wani taron majalisar dokokin kasar, a daidai lokacin da take daf da ba shi wa’adi na 3 a matsayin shugaban ƙasa.
Ga Wani Labarin: Adamawa: Ɗan Takarar Gwamna Na Jam’iyyar LP Ya Janye Wa Aishatu Binani ta APC
Wani karin kasafi a bangaren tsaron ƙasar Sin shi ne mafi girma a duniya, kuma hakan na zuwa ne bayan da ƙasar ta sanar da ƙudirin bunƙasa tattalin arzikinta na kimanin kaso 5 a wannan shekarar.
A cikin kasafin kudin nata na wannan shekara, bangaren tsaro zai samu yuwan tiriliyan 1 da digo 55, kwataankwacin dalar Amurka biliyan 225, wato, ƙarin kaso 7 da ɗigo 2 kenan.
Sai dai har yanzu kasafin kuɗin bangaren tsaron na Sin ƙasa yake da Amurka, wadda ta ware dala biliyan ɗari 8 ga ɓangaren tsaro.
Sai dai wasu masana na ganin ƙasar ta Sin tana kashe sama da abin faɗa a hukumnance.