Rundunar yan sandan jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Kwamishinanta, CP Ibrahim Adamu Bakori, PhD, ta shiga tsakani don dawo da zaman lafiya a kauyen Jajira dake karamar hukumar Ungogo, bayan wasu matasan sun gudanar da zanga-zanga da ka iya tayar da hankali.
Kakakin rundunar yan sandan jihar Kano, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce bayan faruwar lamarin, kwamishinan yan sandan jihar ya tura tawagar jami’an yan sanda ƙarƙashin jagorancin mukaddashin kwamishinan yan sanda ,DCP Lawal Isah Mani, wanda ya gana da jama’ar yankin tare da kwantar musu da hankali
Tunda farko al’ummar yankin Jajiran, sun yi zargin an rufe musu hanya saboda aikin layin dogo da ake gudanarwa, inda suka nuna rashin amincewarsu.
Sanarwar ta ce rundunar ta shirya taron masu ruwa da tsaki na karamar hukumar a hedikwatar ‘yan sanda dake Bompai.
Taron ya samu halattar mataimakin shugaban karamar hukumar Ungoggo , Hon. Auwal Idris Isah da Hakimin Ungoggo, Alhaji Nura Shehu Ahmad da Dagacin Jajira Malam Ibrahim Muhammad da wakilin ma’aikatar Sufuri ta Tarayya da akilin kamfanin dake gudanar da aikin da sauran masu ruwa da tsaki daga garin Jajira dama Ungogo.
A yayin taron, an tattauna matsaloli tare lalubo hanyoyin magance matsalar data faru
Kwamishinan ‘Yan Sanda CP Ibrahim Adamu Bakori ya shawarci jama’ar yankin su zauna lafiya, sannan su guji yin abunda zai tayar da hankalin al’umma.

