Ƴan bindiga sun sace amarya da ƙawayenta a Sokoto

Wasu da ake zargin ’yan bindiga ne sun kai hari a ƙauyen Chacho da ke ƙaramar hukumar Wurno ta Jihar Sokoto, inda suka yi garkuwa da amarya da ƙawayenta da wasu mazauna yankin har mutum 18.

Daga cikin waɗanda aka sace, mutane uku ne suka samu damar kuɓuta, lamarin da ya faru kwana ɗaya kafin ɗaura auren amaryar.

Sanata Ibrahim Lamido, mai wakiltar yankin, ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta jiha da su ƙara kaimi wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

“Wannan abu idan ana ganin shi yana faruwa a ƙauyuka toh nan gaba birni zai shiga, saboda haka a ajiye siyasa a ƙasa, a zo a haɗa kai a yi harkar tsaro.” in ji Sanatan.

Wani mazaunin garin da ya nemi a sakaya sunansa ya bayyana cewa babu wani saƙo ko kira daga masu garkuwan har yanzu.

A cewar mazaunin, “wannan ba shi ba ne karo na farko da irin wannan harin ya faru a yankin ba, domin kusan sau shida kenan da ’yan bindiga suka afka musu, sai dai wannan shi ne mafi muni.”

Wani mazaunin ya ƙara da cewa al’ummar garin na cikin damuwa saboda hare-haren da ke faruwa kusan kullum, kuma ba su da jami’an tsaro sai dai ’yan sa-kai da suke biyansu daga aljihunsu.

“Muna kira ga gwamnati ta kawo dauki, domin halin da muka tsinci kanmu a ciki ya yi muni.” in ji shi.

Matsalar tsaro a Arewa maso Yammacin Najeriya ta ci gaba da zama babbar kalubale ga jami’an tsaro da al’ummar yankin, lamarin da ke barazana ga zaman lafiya da rayuwar yau da kullum.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *