Home » ‘Ƴan sanda sun kama wasu da ake zargin suna yunƙurin kai hari gidan Atiku Abubakar

‘Ƴan sanda sun kama wasu da ake zargin suna yunƙurin kai hari gidan Atiku Abubakar

by Hassan Abdu Mai Bulawus
0 comment
'Ƴan sanda sun kama wasu da ake zargin suna yunƙurin kai hari gidan Atiku Abubakar

‘Ƴan sanda sun kama wasu mutane guda huɗu da ake zargin suna yunƙurin kai hari ga gidan tsohon mataimakin shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar a birnin Yola.

An fara kama ɗaya daga cikin mutanen ne mai suna Jubrila Mohammed, wanda ya amsa cewa shi mamba ne a kungiyar Boko Haram lokacin da suke yunkurin kai harin da misalin karfe 9 na dare ranar Lahadi.

Wata sanarwa da mai taimaka wa tsohon mataimakin shugaban ƙasar Abdul Rasheed Shehu ya fitar, ta ce an samu nasarar kama abokan haɗin bakinsa guda uku.

Sanarwar ta kara da cewa mutanen da ake zargin sun kuma yi yunkurin kai wa kamfanoni masu alaƙa da Atiku Abubakar a Yola da kuma wasu wurare kafin a kama su.

Zuwa yanzu, an miƙa dukkan mutanen da ake zargi hannun sojoji in ji sanarwar domin ci gaba da bincike.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai dake da cikakkiyar rejista da ke da manufa ta ilimantarwa, wayar da kai Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.

Ofishinmu yana nan a kan titin Guda Abdullahi dake Farm Centre a jihar Kano. 

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi