Home » Ɗan Fashi Ya Zare Wayar Ɗan Sanda A Hanyar Caji Ofis

Ɗan Fashi Ya Zare Wayar Ɗan Sanda A Hanyar Caji Ofis

Wani dan fashi ya zare wayar dan sandan da ya je kamoshi a hanyar kai shi hedikwatarsu domin bincike a jihar Osun. 

by Mubarak Ibrahim Mandawari
0 comment

Wani dan fashi ya zare wayar dan sandan da ya je kamoshi a hanyar kai shi hedikwatarsu domin bincike a jihar Osun. 

Ana zargin matashin ɗan shekara 23, mai suna Godwin Emmanuel da aikata fashi da makami ne abin da ya tilasata a je a kamo shi.

A hanyar kai Godwin hedikwatar rundunar ‘yan sanda ta jihar Osun din ne dai ya zare wa wani jami’in ɗan sanda wayar hannunsa yayin da suke zaune tare a cikin motar sintirin.

An kama Emmanuel ne tare da wasu ‘ƴan fashi biyu, Olajide Kareem mai shekrau 28 da Mike Emmanuel mai shekaru 33, waɗanda ake zargi da yi wa mazauna yankin fashi da makami tare da yin lalata da wata mata mai shelaru 65 a hanyar Ilesu zuwa Osun.

Da ya ke gabatar da waɗan da ake zargin a ranar Juma’a, Kakakin rundunar ‘ƴan sandan Jihar Osun, Yemisi Opalola ya bayyana cewa, “ƴan bindigar uku sun yi wa masu ababen hawa da fasinjoji fashin kayayyakinsu inda har su ka harbi wani direban bas a kafarsa wanda daga bisani aka garzaya da shi asibitin Seventh-day Adventist Hospital da ke Ile-Ife inda ya ke samun kulawa.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.
Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi

©MuhasaTVR 2023. Ku nemi izini kafin yin amfani da duk abin da aka wallafa a wannan shafi

Are you sure want to unlock this post?
Unlock left : 0
Are you sure want to cancel subscription?