Mai Martaba Sarkin Rano Alhaji Muhammad Isa Umar ya naɗa tsohon shugaban hukumar shigi da fici ta Najeriya Sanata UK Umar MNI OON Durbin masarautar Rano kuma ɗan majalisar sarki.
An yi naɗin Sanata UK Umar a matsayin Durbin Masarautar Rano ne da safiyar ranar Juma’a a fadar sarkin da ke cikin garin Rano.
Masarautar Rano ta bayyana sanata UK Umar a matsayin jajirtacce kuma ɗan kishin al’ummarsa da ba kasafai ake samun irinsu ba.
- Yau Ce Ranar Kula Da Masu Ciwon Sukari Ta Duniya
- Fatawa Kan Kirifto Na Daga Cikin Fatawa Mafi Wahala Da Nayi-Sheikh Daurawa
Sanata UK Umar ya yi wa mai martaba Sarkin Rano Alhaji Muhammad Isa Umar godiya bisa wannan karramawa.
Ya kuma bayyana Sarkin Rano a matsayin mutumin kirki wanda ya san mutuncin al’ummar da ya ke jagoranta.
Sabon Durbin na Rano ya ce, “Ina da alaƙa mai karfi kuma kyakkyawa da Mai Martaba Sarkin Rano Alhaji Muhammad Isa Umar, amma ba lallai ya san da ita ba.
“Ni ɗan morin sarki ne, lokacin ina yaro ya nuna min ƙauna fiye da yadda duk mutum yake tunani”.
Daga cikin manyan baki da suka halarci bikin naɗin akwai hamshaƙin ɗan kasuwa Alhaji Auwalu Rano, mamallakin kamfanin man fetur na AA RANO da na jiragen sama Rano Air.
An samu baƙi daga ciki da wajen jihar Kano domin taya Sanata UK Umar murnar samun sarautar Durbin Masarautar Rano kuma dan majalisa sarki.