Home » Legas Na Neman Yi Wa Arewa Mulkin Mallaka-Kwankwaso

Legas Na Neman Yi Wa Arewa Mulkin Mallaka-Kwankwaso

by Muhammad Auwal Suleiman
0 comment

‘Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP a zaben 2023 kuma jagoran tafiyar Kwankwasiyya, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya ce akwai shiri mai karfi na yi wa Arewacin Najeriya mulkin mallaka daga jihar Legas. 

Sanata Kwankwaso ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar da jawabi a wurinn taron Jami’ar Skyline a Kano.

Sanata ya yi ikirarin cewa an yi amfani da  Legas wurin rura wutar rikicin masarautu a Jihar Kano.

Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, wanda tsohon gwamnan jihar Kano ne, ya koka kan yadda tabarbarewar tattalin arziki, rashin tsaro, fatara, yunwa da cututtuka iri-iri, su ka yi wa Najeriya dabaibayi. 

Kwankwaso ya ce, “A yau, muna iya gani afili cewa akwai yunƙuri mai karfi  daga ɓangaren Legas na yin mulkin mallaka ga yankin Arewa. Yau, Legas ba za ta bar mu mu zabi sarki ba, komai za mu yi sai an saka mana baki daga Legas.”

Kwankwaso ya kuma yi magana game da karbar haraji, inda ya ce, “A yau muna sane da cewa ana aiki tukuru don dora mana haraji domin a kai Legas.

“kamar yadda muke gani, hatta wayoyin da muke yi ko rajista a nan Kano, ana kokarin kai duk harajin zuwa Legas.

“Hatta ‘ya’yanmu maza da mata da suka kawo masana’antu da yawa a nan Kano da arewacin Najeriya har ma da bankuna, an tilasta musu su mayar da hedikwatarsu Legas saboda harajin ya  tafi Legas.”

Tsohon gwamnan na Kano ya kuma yi tsokaci kan banbance-banbancen da ke tsakanin masu hannu da shuni, inda ya ce, “Mun ga irin kokarin da wasu ke yi na ganin cewa talaka ya kara shiga halin kaka-nika-yi”

A karshe  Kwankwaso ya yi kira ga ‘yan majalisar da suka fito daga yankin Arewacin kasar nan da su farka su tabbatar ba a yi wa yankin magudi ta kowace hanya ba.

“In  kira ga daukacin ‘yan majalisar mu na kasa da su bude ido don kada su bari a yi wani abu da zai cutar da al’ummar Arewacin Najeriya, musamman a nan Kano”.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.
Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi

©MuhasaTVR 2023. Ku nemi izini kafin yin amfani da duk abin da aka wallafa a wannan shafi

Are you sure want to unlock this post?
Unlock left : 0
Are you sure want to cancel subscription?