Home » Rashin Wutar Lantarki Na Neman Hana Gwajin Cututtuka A Kano

Rashin Wutar Lantarki Na Neman Hana Gwajin Cututtuka A Kano

Asibitoci da dama basa iya kula da majinyata masalar da yake janyo a sarar rayuwakan Al’ umma.

by Zubaidah Abubakar Ahmad
0 comment

Matsalar wutar lantarki da ta ki ci, ta ki cinyewa a Najeriya ta fara mummunar illa ga bangaren lafiya a Najeriya. 

Asibitoci da dama basa sun fara gaza kula da majinyata, abin da kr janyo a sarar rayuwaka.

Muhasa ta zaga wasu daga cikin asibitocin da ke birnin Kano domin jin yadda rashin wutar ke shafar harkokin su.

Abubakar Abdulhadi Bako jami’in lafiya ne a daya daga cikin asibitocin sha ka tafi a kano, ya ce ba ƙaramar matsala rahin wutar lantarki ta haifar ba.

Abubakara ya kara da cewa, rashin wutar lantarki ta fara hana yin waya daga cikin gwaje-gwajen da likitoci ke rubutowa marasa lafiya.

Saratu Haruna Yusuf jami’ar lafiya a matakin farko ta bayyana cewa rashin wutar lantarki a Kano ta gurgunta harkar kiwon lafiya.

Yayin zantawar ta da MUHASA, tace, “Wallahi rashin wuta ya shafi harkar lafiya ba kadan ba domin irin halin da mu ke fama dashi har yanxu a sibitin na rashin wuta sai inji mu ke kunnawa shima ba kullum ba”.

Saratu ta yi kira ga gwamnati wurin samar musu da sola domin saukaka aikin su, rage mace-macen da ake samu a harkar lafiya ta hanyar rashin wutar lantarki.

Zainab Gambo Umar, ɗaya daga cikin masu jinya a asibiti ta shaidawa MUHASA cewa tun safe take asibitin babu wutar lantarki daza’awa danta gwajin jinyar da ke damunsa.

Zainab Gambo ta koka akan irin halin da majinyata suke ciki a sibitoci.

Tayi kira ga mahukunta da su taimaka suyi wani abu akan harkar wutar lantarkin domin rashin yin gwaje-gwaje na jawo wasu su rasa rayukansu.

Kafar MUHASA ta kuma tunttubi Abubakar Danjuma Mukadas. masanin a harkar samar da wuta ta hanyar hasken rana, ya bayyana cewa rashin wutar lantarki a harkar lafiya ba karamin haɗari bane.

Ya ce, ya kamata gwamnati ta duba yiwuwar hada asibitoci da sola domin magance matsalar baki daya.

Ya kuma ƙara da cewa ƙasashen da suka ci gaba irin su Jamani, Chana, da India suna amfani da kimiyyar hasken rana domin kaucewa samun matsala.

Abubakar Danjuma Mukadas ya yi kira ga Gwamnatin Najeriya kan ta dubi wannan batu, ya kuma roki gwamnan jihar kano Alhaji Abba Kabir Yusuf da asamawar asibitocin birni da kauye manya da kanana sola saboda gudun samun asarar rayuka da akeyi a dalilin rashin wutar lantarki a sibitoci.

 

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.
Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi

©MuhasaTVR 2023. Ku nemi izini kafin yin amfani da duk abin da aka wallafa a wannan shafi

Are you sure want to unlock this post?
Unlock left : 0
Are you sure want to cancel subscription?