A ranar Juma’a, 20 ga watan Oktoba 2023 aka daura auren Ibrahim Umar Musa Yar’adua da amaryarsa Amira Muhammed Babandede. Ibrahim ɗa ne ga marigayi tsohon Shugaban kasar Najeriya, Malam Umar Musa Yaradua.
Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, shi ne ya waliyin angon, inda gwamnan Jihar Jigawa, Umar Namadi ya wakilci amarya inda aka biya sadaki dubu dari biyar (N500,000) lakadan.
An ɗaura auren ne a lokacin da aka je neman auren a gidan tsohon Shugaban Hukumar Shige da Fice ta Kasa, Muhammed Babandede da ke Birnin Tarayya, Abuja.
Manyan baƙin da suka halarci ɗaurin auren sun haɗa da: Alhaji Dahiru Bara’u Mangal da Barrister Ibrahim Shehu Shema da Senator Abdulaziz Musa Yaradua da Senator Adamu Alero da Alhaji Isah Yuguda da Alhaji Sa’id Dakingari da Alh. Jabiru Tsauri da Alh. Aminu SDY da Hon. Salisu Yusuf Majigiri da Hon. Abdullahi Aliyu Musawa da Sarkin Auyo Baffa Umar wanda ya wakilci Sarkin Hadejia da sauran manyan mutane.