Matatar Man Ɗangote a rage farashin man fetur zuwa N899.50k kan kowace lita albarkacin bukukuwan ƙarshen shekarar 2024.
Babban jami’in kula da sa hannun jari da sadarwa na gamayyar kamfanonin Ɗangote Anthony Chiejina ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a safiyar ranar Alhamis.
Anthony Chiejina ya ce an dauki matakin ne don “sauƙaƙawa ‘yan Najeriya bukatun lokacin hutun ƙarshen shekara”.
- Shugaba Tinubu Ya Jinjina Wa Haƙuri Da Juriyar ‘Yan Najeriya
- An Sace Wayoyi Miliyan 25 A Cikin Shekara 1 A Najeriya – NBS
Matatar man ta kuma nuna jin daɗin ta ga ‘yan Najeriya kan goyon bayan da su ke ba shi musamman lokacin da kasar ke shiga lokacin shagulgulan Kirsimeti da ƙarshen Shekara.