Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa (NBS), ta ce an sace wayoyin salula sama da miliyan 25, daga watan Maris ɗin 2023 zuwa Afrilun 2024.
NBS ta ce wannan sata ta shafi sama da mutum miliyan 17 a tsakanin wannan lokacin.
Ƙididdigar ta NBS na nufin cewa a cikin wayoyi 10 da mutane ke amfani da su, an sace guda bakwai a shekara guda.
- ‘Yan Sanda Na Farautar Sanusi Bature Dawakin Tofa
- An Kashe Mutane Dubu 395,022 A Arewa Daga 2023 Zuwa 2024-NBS
Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa ta kuma ce an fi samun satar wayoyin a gidaje da wuraren taruwar jama’a, kuma kashi 11.7 ne kacal na waɗanda aka yi wa satar suka kai wa ’yan sanda rahoto kuma suka samun taimakon da su ke nema.
Rahoton, ya kuma bayyana cewa ƙasa da kashi 10 na laifin satar wayoyi ne, suka kai gaban ’yan sanda, saboda dalilai daban-daban.
“A matakin ‘yan ƙasa kuwa, kashi 21.4 na ’yan Najeriya ne, suka ce an aikata musu laifin da ya saɓa wa doka, kuma satar waya na daga cikin manyan laifukan, inda yake da kashi 13.8,” in ji rahoton.