Kamfanin labarai na Reuters ya ruwaito cewa matatar man fetur din Dangote da ke jihar Legas ta fara wata tattaunawa da ƙasar Libiya da ake sa ran za ta bada damar fara sayo ɗanyen man da za ta rika tacewa har ganga dubu dari 6 da 50 kullum.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da Hukumar da ke lura da man fetur ta Najeriya NMDPRA ta zargi matatar ta Dangote da samar da man da ba shi da inganci. Zargin da tuni Alhaji Aliko Dangote ya musanta.
Haka zalika, rahotanni daga Angola na tabbatar da cewa attajirin zai fara sayen danyen mai daga kasar domin tacewa a matatarsa dake jihar Legas, kudu maso yammacin Najeriya.
‘Yan Najeriya dai na ci gaba da musayar ra’ayi dangane da wannan turka-turka da ta sako matatar ta Dangote a gaba, a daidai lokacin da su ke tunanin daga ta fara aiki za su samu sauki.