Tsohon mataimakin shugaban Kasar Najeriya Atiku Abubakar ya ce abin takaicin ne yadda ake samun takaddama tsakanin hukumomin harkokin mai da Alhaji Aliko Dangote.
Atiku ya ce, sakacin da ake neman yi da babban kamfani kamar na Dangote a Najeriya, zai sanyaya gwiwar duk wani mai sha’awar kafa wani abu a kasar.
Ya bayyana takaicinsa kan yadda hukumomin gwamnatin Najeriya suka shiga takaddama da attajirin da ya samar da matatar man da ke iya samar da ganga dubu dari 6 da 50 a kullum.
Atiku ya shiga sahun ‘yan Najeriya da ke ta bayyana ra’ayinsu dangane da rashin jituwar da ta kunno kai tsakanin hukumar NMDPRA da matatar man fetur din Dangote a karshen makon da ya gabata.
A halin da ake ciki dai, rahotanni na cewa gwamnatin Najeriya ta shiga cikin maganar dumu-dumu, inda ake zaton ana wani yunkuri ne na kawo karshen rigimar da ta fusata babban attajirin har ya kai ga yi wa NNPCL tayin sayen matatar tasa.
A yammacin ranar Litinin rahotanni sun bayyana cewa Dangote zai fara shigo da danyen mai daga kasar Libiya da kuma Angola, tun da baya samu a Najeriya.
Dambarwar Matatar Man Dangote Babbar Matsalace-Atiku Abubakar
291
previous post