Shugaban Majalisar Wakilan Najeriya Tajudeen Abbas ya ce za a gudanar da bincike kan zargin da ake yi cewa man fetur ɗin da ake samu daga matatar Dangote bai kai kyau da ingancin wanda ake shigowa da shi daga ƙasashen ƙetare ba.
Tajudeen Abbas ya sanar da hakan ne a ziyarar da ƴan majalisar suka kai matatar man ta Dangote a ranar Asabar.
Abbas ya bayyana damuwarsa kan cece-ku-cen da ake tafkawa dangane da ingancin man da ake shigowa da shi Najeriya.
- Shugaban Amurka Joe Biden Ya Hakura Da Takara
- Dan Majalisa Ya Gwangaje ‘Yarsa Da Kyautar Mota Bayan Kammala Sakandire
Alhaji Aliko Dangote, ya tabbatar da cewa kayan sarrafa man fetur da matatarsa ke amfani da su ingantattu ne kuma sun cika duk wata ƙa’idar Najeriya da ma ta ƙasa da ƙasa.