Daga Suraj Na Iya Idris Kududdufawa
Babbar gadar da ake shiga babban birnin Yamai a kasar Nijar ta karye sakamakon mamakon ruwa saman da ake yi samu a yankin.
Gadar ta karye ne tsakanin mahadar jihar Doso da mahadar shiga birnin na Yamai.
Mafiya yawan al’ummar da suke bi ta jihar Doso domin shiga birnin sun hakura da shiga.
- Farfesa Abdullahi (Pakistan) Ya Zama Shugaban NAHCON
- Ba na neman Kujerar Shugabancin Najeriya a 2027 – Ganduje
A yanzu dai haka akwai motocin matafiya a jibge a hanyar sakamakon wannan lamari da ya afku na karyewar gadar.
Akwai mutane daga jihoshi da dama a kasar Niger da sai sun bi ta jihar Doso sannan su isa birnin suma lamarin ya ritsa dasu.