Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama wani da ake zargi da safarar mutane (wanda aka sakaya sunansa) a wani garejin motoci tare da wasu mata 12 da ake zargi da safarar mutane da ke shirin tafiya Legas.
Bayanin hakan ya fito ne daga bakin mataimakin Kwamandan Hukumar ta Hisbah, Sheikh Mujahideen Aminuddeen.
Sanarwar ta bayyana cewa, jami’an rundunar sun kama mutumin ne a wani garejin motoci da ke kan titin zuwa Zariya.
Hukumar ta bakin mataimakin ta bayyana cewa, jami’an Hisbah ƙarƙashin jagorancin OC Muhammad Bashir na garejin motoci sun kama wakilin safarar wanda aka ce ya fito daga Jihar Borno, ya hau mota zuwa Legas tare da waɗanda ake zargin.
Aminuddeen ya bayyana cewa, bayanan farko sun nuna cewa, mutumin yana safarar matan ne, kowannensu yana da fasfo na ƙasa da ƙasa zuwa ƙasar Saliyo ta hanyar Legas, Jamhuriyar Benin da Ghana, inda ya ƙara da cewa mutumin yana da shirin yin biza ga waɗanda ya yi safarar don tafiya ƙasar Saudiyya don neman aiki.
- Matasa Sun Kashe Yan Bindiga 6 Sun Sha Alwashin Kare Kansu
- Yan Sanda Sun Kama Masu Yin Sojan Gona Da Sunan Su A Kano
Aminuddeen ya kuma bayyana cewa, a yayin da ake yi musu tambayoyi, matan sun sanar da jami’an Hisbah cewa kowaccen su ta biya Naira miliyan 1,500,000 a karon farko tare da yarjejeniyar biyan cikon sauran kuɗi idan sun samu aiki a inda za su.
A cewar hukumar, ɗaya daga cikin matan akwai mai shekara 50 sauran biyu kuma akwai mai shekara 23 da mai shekara 20, yayin da ragowar kuma ’yan shekara 15 ne.
Ya bayyana cewa a cikin waɗanda aka yi safarar, uku sun fito daga Katsina, biyu daga Kano, ɗaya daga jihohin Borno, Jigawa da Zamfara.