• Home  
  • 2027: Tinubu da Atiku da Obi za su fafata a muhawarar ƴan takarar shugaban ƙasa
- Babban Labari

2027: Tinubu da Atiku da Obi za su fafata a muhawarar ƴan takarar shugaban ƙasa

An gayyaci Shugaba Bola Tinubu, Atiku Abubakar, Peter Obi da wasu ’yan takarar shugaban ƙasa huɗu domin halartar muhawarar siyasa gabanin zaɓen 2027. Ƙungiyar Political Intelligence Group (PIG) ta Politico.ng ce ta shirya muhawarar, wadda za a gudanar a ranar 10 ga Janairu, 2027, a Abuja. Sauran waɗanda aka gayyata sun haɗa da Seyi Makinde, […]

An gayyaci Shugaba Bola Tinubu, Atiku Abubakar, Peter Obi da wasu ’yan takarar shugaban ƙasa huɗu domin halartar muhawarar siyasa gabanin zaɓen 2027.
Ƙungiyar Political Intelligence Group (PIG) ta Politico.ng ce ta shirya muhawarar, wadda za a gudanar a ranar 10 ga Janairu, 2027, a Abuja.
Sauran waɗanda aka gayyata sun haɗa da Seyi Makinde, Donald Duke da Adewole Adebayo.
Mai shirya taron, Lai Omotola, ya bayyana cewa muhawarar za ta ɗauki tsawon sa’o’i uku, domin bai wa ’yan Najeriya damar tantance manufofi, ƙwarewa da shirye-shiryen ’yan takarar wajen jagorantar ƙasar.
Ya ce za a raba muhawarar zuwa sassa biyar, inda kowane ɗan takara zai samu mintuna biyar domin amsa tambayoyi da mintuna biyu domin mayar da martani.
Omotola ya bayyana cewa manufar shirin ita ce bunƙasa kamfen bisa manufofi da ƙarfafa riƙon amana a tsarin dimokuraɗiyya.
Ya kuma yi kira ga ’yan Najeriya da su guji tashin hankali da rikice-rikicen siyasa yayin da ake tunkarar babban zaɓen 2027

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai

2027: Tinubu da Atiku da Obi

2027: NDC ta zargi APC da