Namadi Ya Kaddamar da Shirin Fadada Ilimi yayin da SLU ta Yaye Dalibai Sama da 4,000

Daga Ali Rabiu Ali, Dutse
Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya bayyana wani gagarumin shirin fadada ilimin manyan makarantu, wanda ya hada da shirin kafa jami’ar likitanci ta musamman da kuma inganta manyan gine-gine, yayin da Jami’ar Sule Lamido (SLU) ta yaye dalibai 4,109 a bikin yaye dalibai na hadin gwiwa.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Asabar a wajen bikin yaye dalibai karo na biyu na jami’ar, inda aka ba dalibai daga zangon karatu shida (2018/2019 zuwa 2024/2025) digiri-digiri daban-daban.
Namadi ya ce gwamnatin jihar na kara kaimi wajen sake fasalin ilimin gaba da sakandare domin ya dace da bukatun zamani, tare da mayar da hankali kan fannonin kimiyya, fasaha da kuma harkokin lafiya.
Daya daga cikin manyan tsare-tsaren shi ne sauya wata jami’a mai zaman kanta da ke Majia a karamar hukumar Taura zuwa jami’a ta musamman kan harkokin likitanci da sauran fannoni masu alaka da lafiya. A cewarsa, an riga an mika shirin gaban majalisar dokokin jihar bayan samun amincewar Hukumar Kula da Jami’o’i ta Kasa (NUC).
“Mun kuduri aniyar tafiyar da jami’ar ne karkashin hadin gwiwar gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu domin tabbatar da dorewa da kuma gogayya a matakin duniya,” in ji gwamnan.
A Jami’ar Sule Lamido, Namadi ya ce ayyukan da ake ci gaba da yi sun hada da kafa Kwalejin Koyar da Likitanci, gina sabbin dakunan kwanan dalibai da ma’aikata, ginin bakin malamai na wucin gadi (sabbatical lodge), da kuma sabon filin taron yaye dalibai.
Ya kara da cewa ana kuma kafa Cibiyar Bincike kan Muhallin Ruwa (Wetland Research Centre) domin magance matsalolin muhalli da bunkasa binciken sauyin yanayi a jihar.
Gwamnan ya bayyana cewa wadannan shirye-shirye na daga cikin babban shirin mayar da jami’ar ta zama daya daga cikin manyan jami’o’in duniya da za su iya gogayya a matakin kasa da kasa.
Haka kuma ya bayyana cewa gwamnatin jihar na ware kaso tsakanin kashi 26 zuwa 30 cikin dari na kasafin kudinta na shekara-shekara ga bangaren ilimi, matakin da ya ce ya taimaka wajen inganta gine-gine, kara yawan dalibai a makarantu da rage yawan yara marasa zuwa makaranta.
Namadi ya kuma yi tsokaci kan gyare-gyaren da ake yi a bangaren koyon sana’o’i da fasaha, inda ya ce an daga darajar manyan makarantun sakandare guda takwas zuwa cibiyoyin kwarewa, tare da sake fasalin Kwalejin Remedial da Advanced Studies da ke Babura domin dacewa da tsarin koyar da sana’o’i na kasa (TVET).
Da yake bayyana ilimi a matsayin ginshikin ci gaba mai dorewa, gwamnan ya jaddada cewa zuba jari a kan dan Adam shi ne hanya mafi inganci ta samun ci gaba mai dorewa da zaman lafiya.
Bikin ya kuma kunshi nadin Sarkin Katagum, Alhaji Umar Faruk II, a matsayin Kansila na biyu na jami’ar.
Haka zalika, an bai wa wasu fitattun mutane uku digirin girmamawa, ciki har da sabon Kansilan, wakilin Qatar Charity Nigeria, da kuma jami’i daga Kungiyar Matasa Musulmi ta Duniya (WAMY).
Gwamna Namadi ya taya daliban murna tare da bukatar su rike gaskiya da rikon amana, su kuma bada gudunmawa mai ma’ana ga al’umma, yana mai tabbatar da cewa gwamnati za ta ci gaba da tallafawa bangaren ilimi ta hanyar hadin gwiwa, bincike da kirkire-kirkire.

Post masu alaƙa

Babandede Ya Ziyarci Iyalan Hon. Laushi, Ya Ba Su Tallafi

Da Fulani Aka Kama da Wuraren ƙera Makamai a Filato, da War Haka Duniya ta Dauka:-Zagazola Makama

Gwamna Bala Mohammed ya canja sheka daga jam’iyar PDP zuwa jam’iyyar APM