Aƙalla mutane kusan 200 ake fargabar sun mutu bayan jiragen soji sun kai hari kan kasuwar a garin Jilli da ke kan iyakar jihohin Borno da Yobe a ƙarshen mako.
Jiragen kai harin ne a yayin wani samamen soja da ke niyyar kai hari kan waɗanda ake zargin ’yan Boko Haram ne a yankin.
Mazauna yankin sun bayyana yadda jiragen yaƙi guda huɗu suka kai harin a lokacin da ake tsaka da harkoki a kasuwar ta mako mako da ke tsakanin ƙananan hukumomin Gubio ta Jihar Borno da kuma Geidam a Jihar Yobe.
A wata sanarwa da kakakin ɓangaren jiragen sama na rundunar Operation HADIN KAI, Sani Uba, ya fitar a ranar Lahadi, ya ce an hallaka ’yan ta’adda da dama, an lalata motocinsu, yayin da sauran suka tsere a lokacin harin.
Sai dai bayan bayyanar rahotannin mutuwar fararen hula, rundunar sojin saman Najeriya ta sanar da fara bincike kan lamarin.
NAF ta ce ta ɗauki zarge-zargen da muhimmanci, inda ta kunna sashen binciken illar da fararen hula ke fuskanta (CHAI-Cell) domin gano gaskiyar abin da ya faru a wajen.
Kasuwar mako-mako ta Jilli na jawo ’yan kasuwa da masu saye daga yankuna da dama, ciki har da Gubio, Futchimiram da Benisheikh a Jihar Borno, da kuma Gurokayeya da Geidam a Jihar Yobe.
Majiyoyi da dama sun ce jirgin yaƙin da ya kai harin na bin diddigin wasu da ake zargin ’yan ta’adda ne da suka je kasuwar domin karɓar haraji daga ’yan kasuwa da kuma samo kayayyaki.
Wani ganau mai suna Umar Bomai ya shaida wa wakilinmu cewa kimanin ’yan kasuwa 200 aka kashe a ƙauyen Jilli da ke yankin Futchimiram na Karamar Hukumar Geidam.
“Lamarin ya faru ne yayin da a daidai lokacin da kasuwar ke ciki da jama’a. Da farko mun ga jirgi ɗaya yana zagayawa sama, muna zaton yana bayar da tsaro. Amma daga baya wasu suka ƙaru har suka kai huɗu.
“Nan take muka ji wata ƙara mai ƙarfi, ba tare da sanin cewa hari ne daga sama ba. Kafin mu ankara, jiragen suka fara jefa bama-bamai, jama’a suka fara guje wa domin tsira.
“Ko da mutane na ƙoƙarin tserewa, harin bai tsaya ba. Mun ƙirga gawarwaki kusan 200 a wurin, kuma mai yiwuwa sun fi haka,” in ji shi.
Yawan mace-mace na iya ƙaruwa
Wani mazaunin yankin, Babagana Bukar, wanda mahaifinsa na cikin waɗanda suka rasu, ya ce adadin na iya zarce 200 yayin da ake ci gaba da gano gawarwaki.
“Yawan waɗanda suka mutu na iya haura 200. Wasu sun mutu a kasuwa, wasu kuma a daji yayin da suke gudu. Hatta a asibiti, mutum 11 daga cikin waɗanda aka kwantar sun rasu yayin jinya. Har yanzu muna ci gaba da tattara gawarwaki,” in ji shi.
Da aka tuntubi kansilan yankin Futchimiram, Malam Lawan Zanna, ya ce kimanin mutum 200 aka kashe, duk da cewa ba a tantance ainihin adadi ba.
Ya ce, “Har yanzu ba mu da cikakken adadin waɗanda suka mutu, amma wani ganau ya tabbatar min da cewa sama da mutum 200 sun rasu.