- Gidauniyar “Renewed Hope” Ta Tallafa Wa Gidaje Marasa Galihu 154,412 A Jigaw
Daga Ali Rabiu Ali, Dutse
Akalla gidaje marasa galihu 154,412 ne aka yi wa rajista domin cin gajiyar tallafin tsaro na zamantakewa na Renewed Hope Social Security Grant a Jihar Jigawa.
Kwamishinan Ma’aikatar Ayyuka na Musamman da Harkokin Jin Kai ta Jihar Jigawa, Hon. Auwal Dalladi Sankara, ne ya bayyana hakan yayin da yake zantawa da manema labarai kan yadda ake gudanar da shirin.
Ya ce ma’aikatar ta fara rabon tallafin ne a mataki na farko tun a watan Janairu, yayin da a yanzu ake gudanar da mataki na biyu na shirin.
A cewarsa, zuwa yanzu gidaje 126,636 daga kananan hukumomi 27 na jihar sun karɓi katin biyan kuɗin tallafin.
Sankara ya bayyana cewa ana sa ran kammala rabon katunan ga sauran gidaje 27,776 cikin lokaci domin tabbatar da cewa talakawa sun amfana da shirin da gwamnatin Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ta ƙaddamar.
Kwamishinan ya ce Shugaba Tinubu ya ƙara yawan kuɗin tallafin daga Naira 10,000 zuwa Naira 25,000 a kowanne zagayen biyan kuɗi na wata biyu-biyu.
Ya ƙara da cewa kowane wanda ya ci gajiyar shirin zai karɓi kuɗin sau uku, wanda jimillarsu ta kai Naira 75,000.
“Shugaban Ƙasa ya yi wannan ƙarin ne domin ƙara tasirin shirin wajen inganta abinci da tattalin arzikin iyalai,” in ji shi.
Ya bayyana cewa duk da cewa adadin kuɗin na iya zama kaɗan a gani, amma yana da matuƙar tasiri ga rayuwar talakawa da kuma ƙananan harkokin kasuwanci a cikin al’umma.
“Idan aka dubi jarin masu sayar da abinci, masu shayi da sauran ƙananan ’yan kasuwa, za a fahimci irin tasirin da wannan tallafi ke yi wajen bunƙasa tattalin arzikin jama’a,” in ji Sankara.
Ya kuma yabawa Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, bisa goyon bayan da yake bai wa shirye-shiryen da ke da nufin inganta rayuwar al’ummar jihar.
A cewarsa, shirin na Renewed Hope Social Security Grant na daga cikin tsare-tsaren gwamnatin Shugaba Tinubu na farfaɗo da tattalin arzikin karkara da kyautata rayuwar jama’a, wanda kuma ya yi daidai da manufofin gwamnatin Malam Umar Namadi na ajandar ci gaban Jigawa mai maki 12.
Sankara ya tabbatar wa al’ummar Jigawa cewa Shugaba Tinubu da Gwamna Namadi na ci gaba da aiki tare domin samar da walwala da ci gaba mai ɗorewa ga jihar da ƙasa baki ɗaya.