KACRAN: Babu wani babban rikicin manoma da makiyaya a Yobe

Ƙungiyar Makiyaya ta Kulen Allah ta Najeriya (KACRAN) ta ce jihar Yobe ba ta samu wani babban rikicin manoma da makiyaya da ya haddasa asarar rayuka ko lalata dukiya ba tun bayan fara kakar noman shekarar 2026.

A cikin wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar bayan wani taron wayar da kan jama’a a Damaturu, KACRAN ta ce ƙara samun haɗin kai tsakanin manoma da makiyaya, tare da ƙoƙarin gwamnatin jihar na tabbatar da zaman lafiya, ya taimaka wajen hana manyan rikice-rikice.

Ƙungiyar ta buƙaci manoma su guji kutsawa cikin wuraren kiwo da aka tanada da kuma hanyoyin da dabbobi ke bi, yayin da ta yi kira ga makiyaya su guji shiga gonakin da aka shuka da kuma lalata amfanin gona.

KACRAN ta kuma buƙaci bangarorin biyu su rika kai rahoton duk wata matsala ga hukumomin da abin ya shafa maimakon ɗaukar doka a hannu ko yin hukuncin gaggawa ba tare da bin ka’ida ba.

Ƙungiyar ta yaba wa Gwamna Mai Mala Buni, sarakunan gargajiya, shugabannin ƙananan hukumomi da jami’an tsaro bisa rawar da suke takawa wajen tabbatar da zaman lafiya a jihar.

Haka kuma, KACRAN ta yi kira ga sauran gwamnonin jihohi da su yi koyi da tsarin Yobe wajen warware rikicin manoma da makiyaya cikin lumana, musamman yayin da ake tunkarar zaɓen shekarar 2027.

Post masu alaƙa

Rundunar yan sandan jihar Kano ta kama wanda ake zargi da garkuwa da mutane,sannan an kwato Drone.

Ƙungiyar kare haƙƙin Musulmi ta buƙaci a biya diyyar masu haƙar ma’adinai 37 da suka rasu Neja

Atiku ya buƙaci Tinubu ya yi bayanin dalilinsa na ƙin halartar taron UNGA karo na uku a jere