CP Ibrahim Bakori ya kai gaisuwar ban-girma ga Sarkin Karaye tare da halartar bikin rantsar da yan NYSC.

Kwamishinan ’yan sandan jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya kai ziyara fadar mai martaba sarkin Karaye, Alhaji Dr. Muhammad Maharaz, inda suka tattauna kan harkokin tsaro da hadin gwiwa tsakanin jami’an tsaro da al’umma.

CP Bakori ya ce ziyarar na daga cikin kokarin rundunar na karfafa aikin ’yan sanda tare da al’umma, bisa umarnin Babban Sufeto Janar na ’yan sandan Najeriya, IGP Olatunji Rilwan Disu.

Ya bukaci sarakunan gargajiya da su ci gaba da bai wa jami’an tsaro hadin kai da shawarwari wajen yaki da aikata laifuka.

Sarkin Karaye ya yaba da kokarin rundunar wajen tabbatar da tsaro, tare da alkawarin ci gaba da ba ta goyon baya.

A yayin ziyarar, CP Bakori ya kuma halarci bikin rantsar da sabbin ’yan bautar kasa na NYSC Batch B, Stream II na 2026, a sansanin NYSC da ke Kusalla Dam, a karamar hukumar Karaye.

Post masu alaƙa

Rundunar yan sandan jihar Kano ta kama wanda ake zargi da garkuwa da mutane,sannan an kwato Drone.

Ƙungiyar kare haƙƙin Musulmi ta buƙaci a biya diyyar masu haƙar ma’adinai 37 da suka rasu Neja

Atiku ya buƙaci Tinubu ya yi bayanin dalilinsa na ƙin halartar taron UNGA karo na uku a jere