Kwamishinan yan sandan jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya sake tabbatar da cewa rundunar za ta ci gaba da bin dokar gudanar da shari’ar laifuka ta Jihar ACJL, tare da kare haƙƙin waɗanda ake zargi da aikata laifi.
CP Bakori ya bayyana hakan ne yayin wani taron horaswa kan shirin PDSS da aka gudanar a Kano tare da haɗin gwiwar hukumar UNDP da kwamitin sa Ido kan aiwatar da dokar tafiyat da shari’un Laifuka.
Ya ce shirin zai taimaka wajen rage cunkoso a a wuraren da ake tsare da mutanen da ake tuhuma da tabbatar da cewa suna samun damar samun lauya, da kuma gudanar da binciken laifukan bisa tanadin doka.
Ya ƙara da cewa rundunar ta horas da jami’anta kan shirin, tare da kafa sashe na musamman a CID Bompai domin tabbatar da cewa ana bin dokar yayin gudanar da bincike.
Masu ruwa da tsaki a ɓangaren shari’a sun yabawa rundunar bisa yadda take aiwatar da shirin, yayin da rundunar ta sake jaddada aniyarta na kare haƙƙin ɗan Adam da tabbatar da adalci ga kowa.