Kano

CP Ibrahim Bakori ya kai gaisuwar ban-girma ga Sarkin Karaye tare da halartar bikin rantsar da yan NYSC.

Kwamishinan ’yan sandan jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya kai ziyara fadar mai martaba sarkin Karaye, Alhaji Dr. Muhammad Maharaz, inda suka tattauna kan harkokin tsaro da hadin gwiwa tsakanin jami’an tsaro da al’umma. CP Bakori ya ce ziyarar na daga cikin kokarin rundunar na karfafa aikin ’yan sanda tare da al’umma, bisa umarnin […]

Read more

Matasa sun ƙona motar jami’an KAROTA a Kano

Wasu fusatattun matasa sun ƙona wata motar aiki ta Hukumar Kula da Zirga-zirgar Ababen Hawa ta Jihar Kano (KAROTA) bayan wani hatsari da ya faru a yankin Kwanar Dawaki da ke kan babbar hanyar Kano zuwa Zariya. Matasan sun zargi jami’an KAROTA da haddasa hatsarin, lamarin da ya sa suka banka wa motar hukumar wuta. […]

Read more

An kama mutum 2 kan zargin sayar da filayen gwamnatin a Kano

Gwamnatin Jihar Kano ta kama wasu mutum biyu bisa zargin rabawa da sayar da filayen gwamnati ba bisa ka’ida ba a yankin Rimin Zakara da ke Ƙaramar Hukumar Ungoggo. Kwamishinan Filaye da Tsare-tsaren Birane na jihar, Alhaji Abduljabbar Muhammad Umar, ne ya bayyana hakan yayin da yake zantawa da manema labarai a Kano. Ya ce […]

Read more