Alarammomi sun amince da tsarin haɗa ilimin boko da na addini a Jigawa

 

Daga Ali Rabiu Ali, Dutse

 

Gwamnatin Jihar Jigawa tare da haɗin gwiwar UNICEF da tallafin Tarayyar Turai (EU), sun fara shirin wayar da kan Alarammomi kan yadda za a haɗa ilimin karatu da lissafi na zamani (Foundational Literacy and Numeracy- FLN) da tsarin karatun Tsangaya, domin ƙara wa Almajirai ilimin rayuwa ba tare da rage darajar karatun Alƙur’ani ba.

 

An gudanar da taron wayar da kan ne ranar Alhamis a Dutse, inda aka gayyaci Alaramma daga ƙananan hukumomin jihar domin fahimtar manufar shirin da kuma rawar da za su taka wajen aiwatar da shi.

 

Da yake jawabi a wajen buɗe taron, Babban Sakataren Hukumar Ilimin Tsangaya ta Jihar Jigawa (JSTEB), Dr. Abubakar Maje Hamisu, ya ce manufar shirin ita ce kawar da ruɗani da rashin fahimta da wasu malamai ke yi game da haɗa ilimin boko da na Tsangaya.

 

Ya ce wasu Alarammomin na ganin cewa shirin zai maye gurbin tsohon tsarin Tsangaya, alhali hakan ba gaskiya ba ne.

“Akwai rashin fahimta da dama game da wannan tsari. Wasu na tunanin za a rushe tsarin Tsangaya ne, amma ba haka ba ne. Maimakon haka, an kawo shi ne domin ƙarfafa tsarin ilimin Tsangaya,” in ji shi.

 

Ya bayyana cewa Almajirai za su ci gaba da koyon Alƙur’ani da ilimin addini, sannan a ƙara musu ilimin karatu, rubutu, lissafi da kuma koyon sana’o’i domin su samu damar rayuwa mai inganci a nan gaba.

 

Dr. Hamisu ya bayyana Alaramma a matsayin ginshiƙin tsarin Tsangaya, yana mai cewa ba tare da cikakken goyon bayansu ba, ba za a samu nasarar aiwatar da shirin ba.

 

Ya kuma buƙaci mahalarta taron da su isar da abin da suka koya ga sauran Alaramman da ba su samu damar halartar taron ba.

 

“Duk abin da kuka koya a nan kada ya tsaya gare ku. Ku koma ku sanar da sauran malamai domin su ma su fahimci manufar wannan shiri. Hakan ne zai taimaka wajen gina ingantaccen tsarin ilimin Tsangaya a Jigawa da ma Arewacin Najeriya baki ɗaya,” in ji shi.

 

A nasa gabatarwar, malami daga Sashen Ilimin Manya da Harkokin Al’umma na Jami’ar Bayero Kano, Dr. Auwalu Halilu, ya bayyana cewa tsarin haɗa ilimi yana nufin bai wa Almajirai damar koyon Alƙur’ani da ilimin addini tare da karatu, rubutu, lissafi, dabarun rayuwa da koyon sana’a ba tare da rage muhimmancin ilimin addini ba.

 

Ya ce manufar shirin ita ce samar da yara masu cikakken ilimin addini da na rayuwar zamani.

 

“Ba mu zo mu maye gurbin ilimin Alƙur’ani ba. Mun zo ne domin mu ƙarfafa shi tare da ba yara ƙarin ilimin da zai amfani rayuwarsu,” in ji Dr. Halilu.

 

Ya ƙara da cewa wannan tsari zai buɗe wa Almajirai ƙofofin samun ilimi, sana’a da ayyukan yi, tare da taimakawa wajen rage talauci, bara da ware yara daga cikin al’umma.

 

A cewarsa, shirin zai kuma taimaka wa Almajirai su fahimci koyarwar addini tare da kalubalen rayuwar zamani ba tare da rasa asalinsu na Musulunci ba.

 

Taron ya kuma tattauna hanyoyin samar da ingantaccen yanayin koyo mai tsaro ga Almajirai, ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin Hukumar Ilimin Tsangaya ta Jigawa, UNICEF da sauran masu ruwa da tsaki, tare da tsara matakan zaɓen masu horaswa, aiwatar da shirin da sa ido kan yadda yake gudana.

 

A ƙarshen taron, Alarammomin da suka halarta sun bayyana gamsuwarsu da shirin, inda suka yi alƙawarin rungumar tsarin haɗa ilimin addini da na boko a cibiyoyin Tsangayarsu domin inganta ilimin Almajirai a faɗin Jihar Jigawa.

Post masu alaƙa

Gwamnati za ta mayar da yara 5,000 makaranta a Jigawa

Ba mu ƙarƙare batun sauya kayan NYSC ba – Ministan Matasa

CP Bakori ya jaddada kudirin rundunar yan sandan Kano na bin dokar tafiyar da shari’un laifuka ACJL.