• Home  
  • An Kai Mahadi Shehu kurkuku
- Babban Labari - Labarai

An Kai Mahadi Shehu kurkuku

Wata Kotu ta ba da umarnin  a tsare  Mahadi Shehu mai sharhi kan al’amuran yau da kullum a gidan yarisaboda wallafa wani bidiyo iƙirarin cewa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sahale wa Faransa kafa sansanin soja a Arewacin Najeriya. A ƙarshen makon da ya gabata ne dai Hukumar Tsaro ta farin kaya DSS  ta […]

Wata Kotu ta ba da umarnin  a tsare  Mahadi Shehu mai sharhi kan al’amuran yau da kullum a gidan yarisaboda wallafa wani bidiyo iƙirarin cewa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sahale wa Faransa kafa sansanin soja a Arewacin Najeriya.

A ƙarshen makon da ya gabata ne dai Hukumar Tsaro ta farin kaya DSS  ta kama Mahadi Shehu a Kaduna, bayan ya wallafa bidiyon da ke iƙirarin cewa Shugaba Tinubu ya bai wa Faransa dama ta kafa sansanin soja.

Bidiyon da aka ce Mahadi ya wallafa daga baya aka goge, an ga wani hafsan sojan Najeriya yana magana da harshen Hausa, da wani sojan ƙasar waje a bayansa.

Mashawarcin Shugaban Ƙasa kan Sha’anin Tsaro Nuhu Ribadu da Ministan Yaɗa Labarai Mohammed Idris sun ƙaryata iƙirarin na Mahadi a matsayin mara tushe, a wani yunkuri na wanke shugaba Tinubu daga zargin.

Binciken da aka gudanar kan bidiyon da Mahadi Shehu ke iƙirarin sojojin Faransa sun je Jihar Borno domin kafa sansanin soji, ba gaskiya ba ne.

A ranar Talata DSS ta gurfanar da Mahadi Shehu a gaban Mai Shari’a Abubakar Lamiɗo na Babbar Kotun Jihar Kaduna, kan zargin taimaka wa ta’ddanci da tayar da hankalin jama’a.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai