• Home  
  • An Tsinci Jariri A Kwali A Kano
- Babban Labari - Labarai

An Tsinci Jariri A Kwali A Kano

Al’ummar unguwar Tudun murtala tagarji sun tsinci wani jariri sabon haihuwa da aka jefar dashi a cikin kwali. 

Al’ummar unguwar Tudun murtala tagarji sun tsinci wani jariri sabon haihuwa da aka jefar dashi a cikin kwali. 

‘Yan anguwan sun bayyana cewa an tsinci jaririn da misalin karfe 2 na daren ranar Asabar a bakin ramin kaura dake tudun Murtala  tagarji a birnin Kano.

Kwamandan  yan bangar yankin da ake kira da operation zaman lafiya vigilante Sulaiman Rabiu dake unguwar t/Murtala tagarji  ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya ce jami’ansu ne suka tsinci jaririn, inda suka ajjiye shi a ofishinsu zuwa wayewar gari kafin daga bisani suka kai shi asibiti aka tabbatar da rasuwar shi kuma suka mishi janaiza kamar yadda addinin musulunci ya tsara. 

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai