• Home  
  • Jam’iyyar NNPP Ta Dakatar Da Sanata Kawu A Kano
- Babban Labari - Siyasa

Jam’iyyar NNPP Ta Dakatar Da Sanata Kawu A Kano

Jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP)  reshen Jihar Kano, ta dakatar da wasu ‘yan majalisarta guda hudu bisa zarginsu da yin zagon kasa ga jam’iyyar.

Jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) reshen Jihar Kano, ta dakatar da wasu ‘yan majalisarta guda hudu bisa zarginsu da yin zagon kasa ga jam’iyyar.

Shugaban jam’iyyar na jihar Alhaji Hashimu Dungurawa ne ya sanar da dakatarwar da yake zantawa da manema labarai a yau Litinin.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) ya rawaito cewa ‘yan majalisar da aka dakatar sun hada da Sanata Abdurrahman Kawu Sumaila da Hon. Ali madakin gini da Abdullahi Sani Rogo da Kabiru Alasan Rurum.

Dungurawa ya ce mambobin sun fara yin abinda bai dace ba hakan ya sanya aka dauki matakin dakatar dasu.

Ya ba da misali da wani taron da Sanata Kawu Sumaila ya gudanar a jami’ar sa da ke Sumaila ba tare da gayyato ‘yan jam’iyyar ba a matsayin wata alama dake nuna adawa da NNPP din.

Ya bayyana cewa za a kafa kwamitin da zai binciki lamarin. Duk da dakatarwar Dungurawa ya ce har yanzu akwai sauran damar tattaunawa, inda ya ce idan dangantakarsu da jam’iyyar ta gyaru  za’a iya ci gaba da damawa dasu a jam’iyyar.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai