• Home  
  • Sojojin Sudan Na Daf Da Kwace Fadar Shugaban Kasa Daga Dakarun RSF – Gidan Talabijin Na Sudan
- Babban Labari - Kasashen Ketare - Labarai

Sojojin Sudan Na Daf Da Kwace Fadar Shugaban Kasa Daga Dakarun RSF – Gidan Talabijin Na Sudan

Jaridar TRT Hausa ta  bayyana cewa Gidan talbijin na Sudan ranar Alhamis ya ce sojojin ƙasar na dab da karɓe iko da Fadar shugaban ƙasar a Khartoum daga hannun dakarun rundunar RSF, lamarin da ya kawo wani babban sauyi a yaƙin da aka yi shekara biyu ana gwabzawa wanda yake barazanar raba ƙasar.

A yammacin ranar Laraba, an yi musayar wuta a kusa da fadar shugaban ƙasar, inda aka ji fashewar abubuwa da kuma hare-haren sama da sojin ta kai tsakiyar Khartoum, kamar yadda shaidu da kamfanin dillancin labaran Reuters suka ruwaito.

Ɓangarorin biyu na soji sun yi juyin mulki a shekarar 2021, lamarin da ya katse shirin miƙa mulki ga farar-hula, kuma yaƙi ya ɓarke a watan Afrilun shekarar 2023 bayan wani sabon shirin miƙa mulki ga farar-hula ya janyo rikici.

Yaƙin ya janyo abin da Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD) ke kira matsalar jinƙai mafi girma a duniya da kuma ƙeta haƙƙin ɗan’adam mai yawa.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai