Hukumar EFCC ta kama babban Akanta-janar na jihar Bauchi, Alhaji Sirajo Mohammed Jaja, kan zargin almundahanar naira biliyan 70.
Binciken Jaridar LEADERSHIP Hausa ya nuna cewa an kama Alhaji Sirajo Mohammed Jaja ne a ranar Laraba a Abuja tare da wasu mutum biyu, Aliyu Abubakar na kamfanin Jasfad Resources Enterprise, a bangaren canjin takardun kudi (BDC) da kuma Sunusi Ibrahim Sambo, mai hada-hadar kuɗaɗen ta na’urar (PoS).
Dukkaninsu sun shiga hannu ne bisa binciken da ake yi na sama da faɗi, karkatar da dukiyar al’umma, da kuma janyo salwantuwar kuɗade da ya kai Naira biliyan 70.
- Sojojin Sudan Na Daf Da Kwace Fadar Shugaban Kasa Daga Dakarun RSF – Gidan Talabijin Na Sudan
- NLC Ta Buƙaci Shugaba Tinubu Ya Mayar Da Fubara Kan kujerarsa
Wani ƙarin zance kan batun, an gano hukumar na kuma bincikar gwamnan jihar Bauchi, Bala Muhammad dukka da hannu kan wannan lamarin.
Tuni dai bincike ya nuna cewa, an fitar da tsabar kudi naira biliyan 59 ta asusun bankuna daban-daban da babban akantan ya buɗe kuma yake gudanar da su a madadin gwamnatin jihar.
Manema labarai sun gano cewa kuɗaɗen an turasu ne ga Abubakar da Sambo inda su kuma suka miƙa tsabar kuɗaɗen ga wasu agent-agent da makusantan gwamnan.
An kuma gano cewa da fari Abubakar da ke gudanar da BDC ya tsallake sharaɗin beli amma an sake cafke shi.
A lokacin da aka tuntuɓi kakakin EFCC Dele Oyewale kan wannan lamarin, ya tabbatar da batun kamun.