Babban Labari
Kasashen Ketare
Labarai
Sojojin Sudan Na Daf Da Kwace Fadar Shugaban Kasa Daga Dakarun RSF – Gidan Talabijin Na Sudan
Jaridar TRT Hausa ta bayyana cewa Gidan talbijin na Sudan ranar Alhamis ya ce sojojin ƙasar na dab da karɓe iko da Fadar shugaban ƙasar a Khartoum daga hannun dakarun rundunar RSF, lamarin da ya kawo wani babban sauyi a yaƙin da aka yi shekara biyu ana gwabzawa wanda yake barazanar raba ƙasar.

