Daga: Muazu Hardawa, Bauchi
Gwamnatin tarayya da hadin gwiuwar gwamnatin jihar Bauchi sun fito da wani shiri na musamnan don ɗauko majinyata daga gidajen su zuwa asibiti a Jihar Bauchi, ganin yadda majinyatan marasa karfi ke fuskantar matsalar zuwa asibitoci neman magani musamnan a cikin dare.
Shirin zai yi aiki tsawon awa 24 wato dare da rana, Kuma tuni aka bude ofis tare da tanadan motocin suna jiran Kiran ko ta kwana daga masu bukatar taimakon gaggawa.
Farfesa Abdulkarim Mairiga shugaban asibitin kwararru na Bauchi da ke BACAS cikin zantawarsa da wakilinmu a kaddamar da Shirin, ya ce majinyaci ko ‘Yan uwansa za su iya kiran lambar 112, ko 07033064032, motar zata zo a dauki majinyacin, musamnan idan ciwon ya zo masa a gaggauce kuma ba shi da halin zuwa asibiti a kan lokaci.
Kuma duk Wanda aka dauko za a masa jinya da magani kyauta tsawon awa 24 kafin ‘yan uwansa su shirya su ci gaba da jinya.
- Gwamnatin Tarayya Ta Samar Da Shaguna A Hadejia
- Arsenal Ta Yi Wasan Kura Da Madrid A Filin Wasa Na Emirates
Doktar Mairiga Abdulkarim yace an tanadi magungunan ko ta kwana da dukkan kayan jinyar taimakon gaggawa da za a yi amfani da su domin bayar da taimakon gaggawa ga majinyacin kyauta.
Shima shugaban Shirin na motocin Majinyata Dokta Sulaiman Abubakar wanda shine Daraktan magance yaduwar cututtuka a maaikatar kiwon lafiya ta jihar Bauchi ya ce wannan shirin an jima da fara gudanar da shi a wasu jihohin Najeriya.
Don haka yanzu suka himmatu don ganin ya iso Bauchi , talakawa sun ci moriya don rage Shan wahala ko mutuwa da marasa galihu ke yi.
Da zarar an kira wannan lambar za a gaggauta dauko marasa lafiya a kai zuwa daya daga cikin asibitoci biyar da aka tanada don aiwatar da Shirin.
Yace mutane za su amfana karkashin Shirin don an tanada mai a motocin da magunguna da likitoci na musamnan don ci gaban Shirin.
Kuma ana Shirin samar da Karin lambobin waya a kowane sashe don amsa Kiran dauko majinyata zuwa asibiti.
Bayan haka Dokta Abubakar ya kara da cewa akwai yiwuwar fadada shirin zuwa kananan hukumomi 20 na jihar Bauchi tare da samar da wasu motocin ɗaukar majinyata da za a ci gaba da aiwatar da Shirin.

