• Home  
  • Rundunar Yan Sandan Kano Ta Fara Binciken Amaryar Da Ake Zargi Da Kashe Mijinta.
- Babban Labari - Labarai

Rundunar Yan Sandan Kano Ta Fara Binciken Amaryar Da Ake Zargi Da Kashe Mijinta.

Rundunar yan sandan jihar Kano ta ce, ta fara gudanar da bincike kan wata sabuwar amarya mai suna ,Saudat Jibril, yar shekaru 18, bisa zarginta da kashe mijinta, Salisu Idris , mai shekaru 30, ta hanyar yi masa kisan gilla da wuka. Kakakin rundunar yan sandan jihar Kano , SP Abdullahi Haruna Kiyawa , ta […]

Rundunar yan sandan jihar Kano ta ce, ta fara gudanar da bincike kan wata sabuwar amarya mai suna ,Saudat Jibril, yar shekaru 18, bisa zarginta da kashe mijinta, Salisu Idris , mai shekaru 30, ta hanyar yi masa kisan gilla da wuka.

Kakakin rundunar yan sandan jihar Kano , SP Abdullahi Haruna Kiyawa , ta cikin wata sanarwa da ya fitar , ya ce’’ lamarin ya faru a unguwar Farawa, da misalin karfe 12:35am 6 ga watan mayu 2025.

SP Kiyawa ya ce bayan karbar korafin kwamishinan yan sandan jihar, Kano CP Ibrahim Adamu Bakori, ya tura dakarun yan sanda zuwa wurin da lamarin ya faru, inda suka kai Salisu Idris, asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano, wanda likita ya tabbatar da rasuwarsa.

Sanarawa ta kara da cewa , yanzu haka wadda ake zargin tana tsare a sashin gudanar da binciken manyan laifuka don fadada bincike akanta, kafin a gurfanar da ita a gaban kotu da laifin kisan kai.

Kwamishina yan sandan ya ce rundunar yan sandan ba zata lamunci aikata laifuka ba , inda ya tabbatarwa da al’ummar jihar cewa za a yi cikakken bincike don yin adalci ga kowa

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai