Rundunar yan sandan jihar Jigawa ta bayyana cewa yanzu haka tana tsare da wani matashi bisa zarginsa da daddatsa mahaifinsa da Adda, wandada hakan ya yi sanadiyar rasuwarsa.
Kakakin ruazndunar yan sandan jihar , SP Shiisu Lawan Adamu , ne ya tabbatar da hakan a wani takaitaccen sako da ya aike wa da MUHASA TVR.
Sanarwar ta ce matashin da ake zargi yana da shekaru 20, amma rundunar bata bayyana sunansa ba ko kuma garin da ya fito.
SP Shisu Lawan ya tabbatar da cewa sun fara gudanar da bincike akansa kuma za su yi wa al’umma Karin haske anan gaba kadan.
- Tsohon Shugaban Kasa Yar’adu’a Ya Cika Shekaru 15 Da Rasuwa.
- Hukumar Gidan Yari A Kano Sun Musanta Zargin Yin Lalata Da Maza