A ci gaba da ƙoƙarinta na tabbatar da kyawawan halaye da kuma samar da zaman lafiya a tsakanin al’umma, Hukumar Hisbah ta Jihar Yobe ta lalata katan 243 na barasa da galan 100 na barasa da aka haɗa a gida, da aka fi sani da sukudaye.
A wata sanarwa da jami’in yaɗa labarai na Hukumar, Adamu Muhammad ya sanya wa hannu, ta ce an lalata barasa a Damaturu, a wani mataki na aiwatar da dokar hana sha da kayan rarraba barasa a jihar.
Shugaban Hukumar Hisbah na jihar, Dokta Yahuza Hamza Abubakar ne ya bayyana cewa aikin ya yi dai-dai da aikin hukumar na aiwatar da dokokin da ke inganta nagarta da kare martabar al’umma.
- Cibiyar Kasafin Kudin Lafiya Ta Afirka (AHBN) Ta Jaddada Bukatar Samar Da kudade A Shirye-shiryen Rigakafi A Kano.
- Tsohon Kwamishinan Yan Sandan Kano CP Sama’ila Dikko Ya Ce Boye Laifin Yaya Ne Ke Rura Rikicin Fadan Daba.
Dokta Yahuza ya nanata ƙudurin hukumar na samar da zaman lafiya, adalci da gyara al’umma, inda ya ce Hisbah ta kuma sasanta tare da warware wasu matsaloli a ayyukan da suka yi a baya-bayan nan.
Ya buƙaci mazauna jihar da su ci gaba da marawa ƙoƙarin hukumar baya wajen tabbatar da kyawawan ɗabi’u da mutuncin jama’a.

