Mai’aikatan tashar Muhasa TVR Kano, sun fuskanci cin zarafi daga wajen wasu ma’aikatan hukumar tsara birane ta jihar Kano wato KNUPDA, lokacin da suke gudanar da aikinsu a ranar Alhamis.
lamarin ya faru ne a unguwar Gandun Albasa karamar hukumar birnin Kano, inda wakilan tashar Muhasa TVR , suka tarar da jami’an hukumar KNUPDA suna rushe wasu wurare da suke kusa da hanya, amma wasu daga cikin ma’aikatan KNUPDA suka hana Yan jaridar gudanar da aikinsu tare cin zarafinsu ta hanyar duka da kuma yunkurin farfasa musu kayan aikinsu.
A cewar wakilan tashar mun tarar ana aikin rusau a Gandun Albasa, kuma mun nemi izini kafin mu fara dauka, amma wasu daga cikin ma’aikatn suka rinka zaginmu tare da duka har da yunkurin fasa mana kayan aiki.
Nura Hassan Bature da kuma Maryam Shafi’u Sabaru, nada daga cikin wadanda suka fuskanci cin zarfin ta hanyar duka ko kuma murde musu hannu.
- Gwamnatin Tinubu Ta Mayar Da Arewa Saniyar ware – ACF
- Gwamna Uba Sani Ya Dakatar Da Kwamishinan Yada Labaran Gwamnatin Kaduna.
Mai Magana da yawun hukumar KNUPDA , Bahijja Malam Kabara, ta bayyana cewa wasu kananan ma’aikata ne da basu da gogewar aiki ne suka aikata wannan abu.
Yan jarida na ci gaba da fuskantar cin zarafi ko barazana a fadin Duniya, yayin da suke gudanar aiyukansu duk da matakan da kungiyoyin yan jarida da na kare hakkin dan adam da kuma majalissar dinkin duniya, suka ce suna dauka don kawo karshen cin zarafin yan jarida.

