• Home  
  • CP Bakori Ya Jagoranci Karawa Wasu Yan Sanda 1,020 Girma A Kano
- Babban Labari - Labarai

CP Bakori Ya Jagoranci Karawa Wasu Yan Sanda 1,020 Girma A Kano

Rundunar yan sandan jihar Kano, bisa jagorancin kwamishinan ta CP Ibrahim Adamu Bakori,  ta karawa jami’anta biyu girma , a matakai dabam-daban. An gudanar da taron Karin girman a wajen shakatawa na manyan jami’an yan sanda dake unguwar Bompai Kano. Kwamishinan yan sandan, ya bukaci yan sandan da suka sami karin girman, y ace wannan […]

Rundunar yan sandan jihar Kano, bisa jagorancin kwamishinan ta CP Ibrahim Adamu Bakori,  ta karawa jami’anta biyu girma , a matakai dabam-daban.

An gudanar da taron Karin girman a wajen shakatawa na manyan jami’an yan sanda dake unguwar Bompai Kano.

Kwamishinan yan sandan, ya bukaci yan sandan da suka sami karin girman, y ace wannan ya  zama babban kalubale a garesu wajen kara jan damarar yaki da masu aikata laifuka a Kano dan samun zaman lafiya.

CP Bakori ya jaddada kudurin rundunar yan sandan Kano na wanzar da zaman lafiya da kare dukiyar al’ummar baki daya.

Wasu daga cikin ‘yan sandan da aka manna musu mukaman nasu na karin girma sun bayyana farin cikin su akan wannan ci gaba da suka samu.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000