• Home  
  • NSCDC Ta Kama Mutane 3 Da Zargin Halaka Jami’insu A Jigawa
- Babban Labari - Labarai

NSCDC Ta Kama Mutane 3 Da Zargin Halaka Jami’insu A Jigawa

Hukumar tsaron civil defense reshen jihar Jigawa, ta samu nasarar kama wasu daga cikin mutane da ake zargi da yin amfani da Adduna da Gatari wajen halaka wani jami’in hukumar mai suna Bashir Adamu Jibrin. Kakakin hukumar tsaron Civl defense reshen jihar Jigawa, Badruddeen Tijjani Mahmud, ne ya tabbatar da hakan, inda ya ce lamarin […]

Hukumar tsaron civil defense reshen jihar Jigawa, ta samu nasarar kama wasu daga cikin mutane da ake zargi da yin amfani da Adduna da Gatari wajen halaka wani jami’in hukumar mai suna Bashir Adamu Jibrin.

Kakakin hukumar tsaron Civl defense reshen jihar Jigawa, Badruddeen Tijjani Mahmud, ne ya tabbatar da hakan, inda ya ce lamarin ya faru ne lokacin da jami’ansu suke gudanar da aiyukansu.

A cewarsa wasu batagari ne suka yi amfani da Adduna da Gatari suka datsa kansa, a kasuwar Shuwarin dake jihar lokacin da sukaje don kama wasu da ake zargi da aikata laifuka.

Marigayin dan asalin jihar Kano, ne inda yanzu haka aka dawo da gawarsa zuwa ga danginsa don yi masa sutura kamar yadda addinin musulinci ya tanada.

 

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai