• Home  
  • Gwamnatin Katsina Tabbatar Da Ceto Mutane 76
- Babban Labari - Labarai

Gwamnatin Katsina Tabbatar Da Ceto Mutane 76

Gwamnatin jihar Katsina ta ce sojojin Najeriya sun kai samame, inda suka samu nasarar tarwatsa maɓoyar ɗanbindiga Babaro tare da ceto mutum 76 da aka yi garkuwa da su. A wata sanarwa da kwamishinan tsaron cikin gida na Katsina, Nasir Mu’azu ya fitar, ya ce Babaro da yaransa ne suka kai hari a Gidan Mantau […]

Gwamnatin jihar Katsina ta ce sojojin Najeriya sun kai samame, inda suka samu nasarar tarwatsa maɓoyar ɗanbindiga Babaro tare da ceto mutum 76 da aka yi garkuwa da su.

A wata sanarwa da kwamishinan tsaron cikin gida na Katsina, Nasir Mu’azu ya fitar, ya ce Babaro da yaransa ne suka kai hari a Gidan Mantau da ke ƙaramar hukumar Malumfashi ta jihar Katsina.

Ya ce, “sojojin saman Najeriya ne suka kai harin ta sama a tsaunin Pauwa da ke ƙaramar hukumar Kankara, inda suka samu nasarar ceto mutum 76 ciki har da mata da ƙananan yara.”

Kwamishinan ya ce tsaunin ne babban sansani kuma maɓoyar ɗanbindigar, inda ya ke shirya kai hare-hare zuwa garuruwa.

Sai dai kwamishinann ya ce an wani ƙaramin yaro ya rasu, sannan ya ƙara da cewa nasarar da suka samu na cikin yunƙurin da gwamnatin jihar ke yi wajen tabbatar da tsaro a jihar.

A ƙarshe ya yaba wa sojojin Najeriya bisa jajircewar da ya ce suna yi wajen gudanar da aiki ba tare da gajiyawa ba.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000