• Home  
  • Yan Sanda A Kano Sun Kama Barayin Motoci
- Babban Labari - Labarai

Yan Sanda A Kano Sun Kama Barayin Motoci

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kano, ta samu nasarar cafke wasu mutane biyu da ake zargin masu satar motoci ne tare da gano motoci uku da aka sata a wurare daban-daban. A sanarwa da rundunar ta fitar ranar Talata, , ta bayyana cewa ta cafke mutanen biyu tare da wata motar Siena Bus a karamar hukumar […]

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kano, ta samu nasarar cafke wasu mutane biyu da ake zargin masu satar motoci ne tare da gano motoci uku da aka sata a wurare daban-daban.

A sanarwa da rundunar ta fitar ranar Talata, , ta bayyana cewa ta cafke mutanen biyu tare da wata motar Siena Bus a karamar hukumar Wudil bayan samun bayanan sirri daga wani mai kishin ƙasa.

Rundunar ta ce za a gurfanar da wadanda ake zargi a kotu bayan kammala bincike, sannan za a mika motoci ga masu su.

Kwamishinan ‘Yan Sandan CP Ibrahim Adamu Bakori, ya yaba da jajircewar jami’an rundunar tare da gode wa jama’a bisa goyon bayan da suke bayarwa wajen bayar da bayanan sirri.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000