• Home  
  • Gawar Tsohon Mataimakin Gwamnan Nasarawa Ta Iso Najeriya Daga Masar
- Babban Labari - Labarai - Ta'aziyya

Gawar Tsohon Mataimakin Gwamnan Nasarawa Ta Iso Najeriya Daga Masar

Gawar tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar Nasarawa kuma tsohon ƙaramin Ministan Birnin Tarayya (FCT), Sanata Solomon Aku Ewuga, ta iso Najeriya daga kasar Masar inda ya rasu yana da shekaru 70.

Gawar tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar Nasarawa kuma tsohon ƙaramin Ministan Birnin Tarayya (FCT), Sanata Solomon Aku Ewuga, ta iso Najeriya daga kasar Masar inda ya rasu yana da shekaru 70.

Ewuga, wanda ya wakilci jihar Nasarawa ta Arewa a Majalisar Dattawa ta 7, ya rasu ne a ranar Talata, 23 ga Satumba, 2025.

Gawar Ewuga ta iso Najeriya ne a ranar Alhamis ta filin jirgin saman kasa da kasa na Nnamdi Azikiwe, Abuja.

Tawaga daga gwamnatin Jihar Nasarawa karkashin jagorancin Mataimakin Gwamna, Dakta Emmanuel Agbadu Akabe, ta kasance a wurin domin karɓar gawar marigayin.

Haka kuma, an hangi tawagar ƙungiyar yaren marigayin ta Eggon Cultural Development Association (ECDA) da kuma tsohon ɗan takarar gwamna a jam’iyyar PDP, Dakta Emmanuel David Emmanuel (Davematics), a wurin tarbar gawar.

 

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000