Home » Yadda Zaman Majalissar Shura Da Malam Triumph Ya Kasance A Asirce.

Yadda Zaman Majalissar Shura Da Malam Triumph Ya Kasance A Asirce.

Kwamitin shura na jihar Kano ya gudanar da wani zaman jin bahasi da ɗaya daga cikin sanannun malaman addinin Musulunci na jihar, Lawan Triump bayan zargin da aka yi masa na yin kalaman

by Mujahid Wada Guringawa
0 comment

Kwamitin shura na jihar Kano ya gudanar da wani zaman jin bahasi da ɗaya daga cikin sanannun malaman addinin Musulunci na jihar, Lawan Triump bayan zargin da aka yi masa na yin kalaman da ba su dace ba a lokacin zaman karatu.

Sheikh Lawan ya ce yana kira ga waɗanda suka yi ta yaɗa maganganun da su riƙa sauraron karatu cikakke kafin su yanke hukunci.

Wannan tattaunawa tana gudana ne a cikin sirri a Ofishin Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) kuma ya samu halarcin fitattun malaman Musulunci na Jihar Kano.

“Waɗanda ransu ya ɓaci, ina so su fahimci abin da nake nufi, kuma ina musu nasihi da cewa idan suna so su yi wa mutum hukunci, to su ji zancensa cikakke kamar yadda Allah ya yi umarni.

“Waɗanda suka yi aikin jefa mutane cikin damuwa kuma, na san akwai waɗanda ba da gangan suka yi ba, ina roƙon allah ya yafe mana baki ɗaya, akwai kuma waɗanda na san da wasu manufofi suka yi, idan suna da rabon shiriya, Allah ya shirya su.”

Ya ce daga cikin zaluncin da za a yi wa mutum akwai “ɗaukar abin da ya fi so a ce ya muzanta shi.

Allah ya sani babu abin da na fi so kamar zaman lafiya da kwanciyar hankali da haɓakar tattalin arziki, kuma babu wanda yake cin moriyar zaman lafiya kamar malami saboda sai da zaman lafiya ne al’umma za su fahimci karatu.”

A ƙarshe ya yi addu’ar Allah ya saka wa “gwamna da alheri, Allah ya yi wa wannan kwamitin jagora, ya ba su ikon sauke wannan nauyin.

Allah ya sa da jagororancinsu da shawarwarin da za su riƙa ba gwamnati al’umaran Kano su yi kyau.”

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.
Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi

©MuhasaTVR 2023. Ku nemi izini kafin yin amfani da duk abin da aka wallafa a wannan shafi

Are you sure want to unlock this post?
Unlock left : 0
Are you sure want to cancel subscription?