• Home  
  • NOA Ta Rushe Rundunar Yaki Da Rashin Da’a Ta War Against Indiscipline(WaI) Brigade
- Babban Labari

NOA Ta Rushe Rundunar Yaki Da Rashin Da’a Ta War Against Indiscipline(WaI) Brigade

Hukumar wayar da kan jama’a ta kasa NOA, ta rushe rundunar sa kai ta War Against Indiscipline(WaI) Brigade, bayan amincewar majalisar zartarwa ta kasa, sannan ta maye gurbinta da Sabuwar Wata runduna mai suna Citizens Values Brigade. Bayanin hakan yana kunshe a cikin Wata sanarwa da Daraktan sadarwa da yada labarai, Bala Musa, ya rabawa […]

Hukumar wayar da kan jama’a ta kasa NOA, ta rushe rundunar sa kai ta War Against Indiscipline(WaI) Brigade, bayan amincewar majalisar zartarwa ta kasa, sannan ta maye gurbinta da Sabuwar Wata runduna mai suna Citizens Values Brigade.

Bayanin hakan yana kunshe a cikin Wata sanarwa da Daraktan sadarwa da yada labarai, Bala Musa, ya rabawa manema labarai.

Darakta Janar na hukumar NOA, Mallam Lanre Issa-Onilu, ya ce daukar matakin ya dace da tsarin Demokuradiya domin gwamnati ba zata ci gaba da amfani da yaki da rashin da’a a mulkin farar hula ba.

Hukumar wayar da kan jama’a ta kasa NOA ta ce zata fitar da sabbin ka’idojin yadda za a tsara da kuma gudanar da sabuwar rundunar ta Citizens Values Brigade tare da bai wa tsoffin mambobin damar shiga sabuwar rundunar.

NOA ta ce sabuwar rundunar Citizens Values Brigade zata fara aiki ne a makarantun Primary da Sakandire da mambobi dubu 37, 000 daga dukkan jahohin kasar 36 harda babban birnin tarayya Abuja, don inganta halaye nagari a tsakanin al’umma.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000