• Home  
  • Hamɓararren shugaban Guinea Bissau ya isa Senegal
- Babban Labari - Labarai

Hamɓararren shugaban Guinea Bissau ya isa Senegal

Hamɓararren shugaban ƙasar Guinea Bissau ya isa makwabciyar ƙasarsa, Senegal bayan wata yarjejeniya da kungiyar ECOWAS ta jagoranta. Wakilin BBC ya ce ma’aikatar harkokin wajen Senegal ta ce a ranar Alhamis da yamma wani jirgin sama na soji ya sauka a ƙasar da Mista Embalo a ciki. A shekaran jiya Laraba ne sojoji suka hamɓarar […]

Hamɓararren shugaban ƙasar Guinea Bissau ya isa makwabciyar ƙasarsa, Senegal bayan wata yarjejeniya da kungiyar ECOWAS ta jagoranta.

Wakilin BBC ya ce ma’aikatar harkokin wajen Senegal ta ce a ranar Alhamis da yamma wani jirgin sama na soji ya sauka a ƙasar da Mista Embalo a ciki.

A shekaran jiya Laraba ne sojoji suka hamɓarar da Umaro Sissoco Embaló, da sauran jami’ai daga mulki – kwana ɗaya kafin bayyana sakamakon zaben shugaban ƙasar da aka yi.

Da dama na ganin Mr Embaló ne zai yi nasara a zaben na kasar ta yammacin Afirka.

An rantsar da shugaban rundunar sojin ƙasa ta ƙasar a matsayin shugaba na abin da sojojin suka kira gwamnatin rikon-ƙwarya.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai