An janye Yan sanda 11,566 Daga Yi Wa Manyan Mutane Rakiya – Egbetokun

Babban Sufeton ’yan sandan Najeriya, Kayode Egbetokun, ya ce sun janye ’yan sanda 11,566 da ke rakiyar manyan mutane kamar yadda Shugaban Ƙasa ya ba da umarni a kwanakin baya.

Ya kuma ce an sake tura waɗannan jami’an zuwa muhimman wuraren da aka fi buƙatars su don kare al’ummomi masu rauni a fadin ƙasa.

Aminiya ta rawaito cewa Shugaba Bola Tinubu, a ranar Lahadi, ya bayar da umarnin janye jami’an ‘yan sanda daga aikin tsaron manyan mutane tare da umartar a sake tura su zuwa ayyukan tsaro na asali.

Umarnin ya biyo bayan taron tsaro da aka gudanar a Abuja tare da shugabannin rundunonin tsaro da shugaban hukumar tsaro ta DSS.

Yayin da yake jawabi a hedikwatar ’yan sanda da ke Abuja, ranar Alhamis, lokacin da ya gana da manyan jami’an ‘yan sanda masu mukamin kwamishina, Egbetokun ya ce jami’an da aka janye za a mayar da su ga ayyukan tsaro na asali.

Ya ce shawarar janye jami’an daga aikin tsaron mutanen ba ta samo asali daga son rai ba, sai dai daga bukatar gaggawa ta karkatar da ma’aikata zuwa wuraren da tsaron jama’a ya fi bukata.

A cewarsa, wannan mataki ya yi daidai da babban aikin Hukumar ‘Yan Sanda ta Najeriya, wato kare ‘yan ƙasa, al’ummomi da kuma tabbatar da zaman lafiya, yana mai jaddada cewa dukkan jami’an 11,566 da aka janye an sake tura su wuraren aiki.

“A bisa umarnin Shugaban Ƙasa, mun janye jami’an 11,566 daga aikin tsaron manyan mutane. Waɗannan jami’an za a sake tura su zuwa muhimman ayyukan tsaro nan take,” in ji shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *