• Home  
  • ADC ce kawai za ta ceto Najeriya – Atiku
- Babban Labari - Labarai

ADC ce kawai za ta ceto Najeriya – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar ya ce jam’iyyar ADC ce kawai za ta iya ceto Najeriya daga halin da take ciki na matsalar tsaro da tattalin arziki. Yayin da yake jawabi a wurin taron ƙaddamar ofishin jam’iyyar a jihar Taraba a ranar Asabar, Atiku ya ce ya shiga jam’iyyun APC da PDP a baya […]

Tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar ya ce jam’iyyar ADC ce kawai za ta iya ceto Najeriya daga halin da take ciki na matsalar tsaro da tattalin arziki.

Yayin da yake jawabi a wurin taron ƙaddamar ofishin jam’iyyar a jihar Taraba a ranar Asabar, Atiku ya ce ya shiga jam’iyyun APC da PDP a baya kuma ya fahimci ba za su iya fitar da Najeriya daga halin da take ciki ba.

A cikin makon nan ne dai tsohon ɗan takakarar shugaban ƙasar ya yanki katinsa na ADC, lamarin da ke alamta shigarsa jam’iyyar a hukumance.

Atiku Abubakar ya kuma yi kira ga mutanen Taraba su fito su shiga jam’iyyar ta ADC, idan har suna son ”ceto tsaro da tattalin arzikin Najeriya”.

”Ina kira ga mata da matasa, su fahimci cewa muna yin wannan domin inganta makomarsu”, in ji Atiku.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000