Rundunar yan sandan jihar Kano, ta bayyana cewa zata tabbatar da sake jaddada dokar da ta haramta ɗaukar fasinja a kan kowanne irin babur, tare da takaita zirga-zirgar adaidaita sahu daga ƙarfe 10 na dare zuwa 6 na safe.
Dokar, wadda Gwamnatin Jihar Kano ta riga ta sanar da ita tun a baya, ta shafi kanana hukumomin da suka hada da, karamar hukumar Birni da Gwale da Dala da Fagge da Nassarawa da Tarauni da Kumbotso da Ungogo da karamar hukumar Dawakin Kudu da unguwannin Tamburawa da Gurjiya da Jido).
Hakan n kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar CSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya raba wa manema labarai
Rundunar ta ce an baiwa tawagar jami’an tsaro ikon kama wa da bincikar duk wanda ya karya wannan umarni, tare da magance yada labaran karya da ka iya tayar da hankalin jama’a.
Rundunar ta kuma nuna cewa matakan an ɗauke su ne domin ƙara tabbatar da tsaro a fadin jihar, sannan duk wanda aka samu ya keta dokar zai fuskanci hukunci.
- Gwamnatin Kano ta jaddada dokar hana sana’ar Achaɓa
- Ƴan bindiga sun sace amarya da ƙawayenta a Sokoto
Kwamishinan ’Yan Sanda na Jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya bukaci al’umma da su bi ka’idojin, tare da kai rahoton duk wani abu da ake zargin ka iya tada hankalin al’umma a ofishin ’yan sanda mafi kusa ko kuma ta layukan gaggawa na rundunar.
Rundunar ta ce zata yi aiki tare da sauran hukumomin tsaro da hukumar KAROTA domin tabbatar da bin doka da kare rayuka da dukiyoyin jama’a.

