An kama wasu mutum huɗu da ake zargin ’yan bindiga ne ɗauke da makamai da ake zaton bindigogi ne a tashar mota ta Ƙofar Ruwa da ke Jihar Kano.
Tashar motar, wadda ke kusa da kasuwar kayan gini ta Ƙofar Ruwa a Ƙaramar Hukumar Dala.
A cewar mazauna yankin, an kama mutanen ne lokacin da suke ƙoƙarin shiga mota domin tafiya zuwa wani waje a cikin Kano.
“Mutanen da ke tashar motar ne suka lura da makaman da suke ɗauke da su. Take suka gaggauta sanar da jami’an tsaro, waɗanda suka kama s, Su huɗu ne gaba ɗaya,” in ji Musa Balarabe, wani mazaunin yankin.
Ya ce an kama su ne da misalin ƙarfe 1 na rana.
Da farko an kai su ofishin ’yan sanda na Ƙofar Ruwa, kafin daga bisani aka mayar da su ofishin Dala.
Wani mazaunin yankin, Umar Nuhu, ya ce yana cikin shagonsa da ke Kwanar Taya, kusa da ofishin ’yan sandan, lokacin da aka kawo mutanen.
Ya ce hakan ya jawo firgici, inda mutane suka fara gudu a ko’ina.
- Yan Sanda Sun Sake Jaddada Dokar Hana Achaba A Wasu Kananan Hukumomin Kano
- Gwamnatin Kano ta jaddada dokar hana sana’ar Achaɓa
Nuhu, ya ƙara da cewa mutane da yawa sun yi dandazo a ofishin ’yan sandan, yayin da wasu matasan ke son ɗaukar doka a hannu.
Da aka tuntuɓi kakakin ’yan sandan Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa, bai ce komai kan lamarin ba.
Ya ce har yanzu suna tattara bayanai kafin su fitar da sanarwa.
Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, babu wata sabuwar sanarwa daga rundunar ’yan sandan jihar.
Tashar Kofar Ruwa, tasha ce da ke jigilar fasinjoji zuwa jihohi irin su Katsina, Jigawa, Sakkwato, Zamfara, Kebbi, har ma da Jamhuriyar Nijar.
Wannan na zuwa ne daidai lokacin da Jihar Kano ke fama da hare-haren ’yan bindiga, musamman a yankunan da ke da iyaka da Jihar Katsina.
AMINIYA
